Hukumomi a jamhuriyar Niger sun bada tukuici ga masu bada gudummuwar jini, ta hanyar tankade da rairaye da aka gudanar a hukumar kiwon lafiya ta jahar Damagaram, a karkashin jagorancin wakilin gwamnan jahar, da daraktan kiwon lafiya.
A cewar shugaban kwamitin dake kula da shirin, Alhaji Umaru Isa, kimanin takardu dari da bakwai na masu bada jini suka samu, inda bayan nazarin lokutan da suka bada gudummuwar jin ga mabukata, Bage Salisu ya zo na fari saboda ya bada jini sau arba'in da takwas,
Wannan bada jinin na taimakawa ainun, kasancewar ko da yaushe asibitoci na sanarwar neman jini saboda irin matsalar jinin da suke fama da ita, kamar yadda Abu Yahaya darakta na hukumar kiwon lafiya ta jahar Damagaram ya ce, ya kuma yi kira ga gwamnati ta yi wannan tsari a dukkan jahohi, hakan zai rage matsalar karanci jinin.
A nata bangaren, kungiyar masu bada jinin, a ta bakin shugaban ta Mahaman Nuru yace godiya suka yi ga hukumomi da wannan tukuici, ya kuma ce hakan ya kara musu karfin gwiwa, yayin da shi kuma Bage Salisu da ya samu tukuicin ya ce ya fi shekara talatin yana bada jini, tun daga Niamey har aka bude cibiyar bada jini ta Damagaram a shekara ta dubu biyu da bakwai, ya kara da yin kira ga jama'a su dinga bada gudummuwar jini don ceton rai, tare da yin godiya ga gomnati.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum