Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Kungiyoyin Kare Kakkin Mata Sun Yi Kira Da Ayi Zabe Cikin Zaman Lafiya


Zaben Nijar 2021
Zaben Nijar 2021

Matan kun yi kira ga magoya bayan wadanan ‘yan takara na shugaba Mahamad Bazoum da Alhaji Mamane Ousman su kasance masu nuna halin dattako don ganin an gudanar da zabe cikin yanayin zaman lafiya.

Zazzafan kalaman dake fitowa daga bakin ‘yan takarar 2 da magoya bayan su a wannan lokaci na yakin neman zabe a yayinda masu amfani da kafafen sada zumunta ke amfani da kalamai masu daci a mahawarar da suke tafkawa a game da zaben na ranar 21 ga watan fabrerun da muke ciki ne ya sa kungiyoyin kare hakkin mata fitar da sanarwar hadin guiwa don jan hankulan bangarori akan mahimmancin zaman lafiya.

Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.
Masu Aikin Sa Ido a Zaben Nijar Daga Kasashen Afirka.

A na su bangare ‘yan takara na ci gaba da zagaya jihohi inda a jiya lahadi dan takarar PNDS Tarayya Bazoum Mohamed da mukarrabansa suka jagoranci gangami a Zinder, shi kuwa Mahaman Ousman da nasa baradan sun yi nasu gangamin a jiyan a garin Say dake jihar Tillabery a wani lokacin da ya rage kwanaki 4 kacal a rufe yakin neman zabe yayinda hukumar zabe a nata bangare ke ci gaba da horarda jami’anta akan dubarun tafiyar da sha’anin zabe.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti:

Gamgamin Zaman Lafiya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG