Annobar COVID 19 ta jefa ma’aikatan jinya da dama cikin yanayin da basu taba fuskanta ba. Kama daga fama da matukar gajiya, da fargaba, da bacin rai, da kuma nakasa. Wadannan kadan ne daga cikin yanayin da ma’aikatan jinya suka shiga sabili da annobar Korona da duniya ke fuskanta.