Ziyarar Shugaba Trump Ta Biyu a Texas

Shugaba Amurka yana tattaunawa da wasu yara a birnin Houston na jihar Texas, yayin ziyarar da ya kai ta biyu don ganawa da wadanda guguwar Harvey ta shafa. Ranar 2 ga watan Satumbar 2017.

Shugaba Donald Trump ya kwashe yinin jiya Asabar yana ziyarar mutanen da guguwar Harvey ta shafa a jihar Texas inda ya kuma yada zango a sauran sassan da guguwar ta shafa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kwashe yini guda yana ziyartar wadanda bala’in guguwar Harvey ta rutsa da su a jihar Texas, inda ya kuma yada zango a yankin Lake Charles da jihar Louisiana.

Shugaban na Amurka bai yi wani jawabi a baina jama’a ba, amma ya gana da wadanda guguwar ta shafa, inda ya yi musu alakwarin cewa gwamnati za ta kawo musu daukin gaggawa.

A karshen makon da ya gabata ne guguwar Harvey ta sauka a jihar ta Texas, inda ta daidaita yankunan da ke gabar tekun jihar, sannan ta zubar da ruwan saman da ba a taba ganin irinsa ba, a kudu maso gabashin jihar da kuma wasu yankunan jihar Louisiana da ke makwabtaka da Texas.

A farkon ziyarar tasa, shugaba Trump ya yi jawabi a gaban wani taron mutane da suka hadu a gaban wata mujami’a da ake kira First Church Pearland.

Wannan ce dai ziyarar Trump ta biyu a jihar ta Texas cikin mako guda, wacce ta maida hankali wajen yin jaje ga mutanen da suka tsira daga guguwar a birnin Houston.

Uwargida Melania Trump ce ta rufawa mijinta baya a lokacin wannan ziyara wacce ya kai a jiya Asabar.

A halin da ake ciki rahotannin daga jihar ta Texas, suna nuni da cewa adadin mutanen da suka mutu sanadiyar wannan guguwar ya zuwa yanzu ya karu, inda ya kai 44.