Ziyarar Shugaban Chadi Janar Mahamat Idriss Deby A Najeriya

Lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi wa Janar Mahamat Deby Iso (Twitter/ @BashirAahmad)

A ranar 10 ga watan Mayu, Janar Deby, dan shekara 37, ya kai ziyara Nijar, wacce ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar waje tun bayan da ya gaji mahaifinsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Janar Mahamat Idriss Deby, shugaban rikon kwaryar gwamnatin wucin gadi a Chadi.

Deby ya kai ziyarar ce a ranar Juma’a inda bayanai suka yi nuni da cewa shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro a yankin Sahel.

A ranar 19 ga watan Afrilu Deby ya gaji mahaifinsa Idriss Deby Into, wanda ya mutu sanadiyyar raunuka da ya ji yayin da ya kai wa dakarun kasar ziyarar a fagen daga, inda suke fafatawa da ‘yan tawaye FACT,.

Karin bayani akan: Mahamat Deby, Idriss Deby, FACT, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, Jamhuriyar Nijar, kasar ta Chadi, Chad, Nigeria, da Najeriya.

A ranar 10 ga watan Mayu, Janar Deby, dan shekara 37, ya kai ziyara Nijar, wacce ita ce ziyararsa ta farko zuwa kasar waje tun bayan da ya gaji mahaifinsa.

Najeriya, Nijar da Chadi da ke yankin Sahel, na fama da matsalolin tsaro da suka hada na ‘yan ta’adda, ‘yan tawaye da kuma ‘yan fashin daji.