Mataimakin shugaban kasar Najeriya Frafesa Yemi Osinbajo, ya gana da masu ruwa da tsaki kan lamuran kanana da matsakaitan masana’antu a Kano, karkashin shirin gwamnatin tarayya na bunkasa harkokin kasuwanci da samar da rance ga kanana da matsakaitan masana’antu.
Shirin na gwamnati na da manufar samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa ta hanyar raya kananan sana’o’I da masana’antun sarrafa abubuwan bukata domin habaka tattalin arzikin Najeriya.
A yayin ganawar, masu kananan masana’antun sun yi musayar fasaha da mataimakin shugaban na Najeriya ya kan yadda suke muradin gwamnati ta tallafawa harkokin su domin cimma nasara.
Matasa mata da kuma kungiyoyin masu sana’o'I daban daban kimanin dubu talatin ne ake sa ranzasu ci gajiyar samun jari karkashin shirin na gwamnatin Najeriya da mataimakin shugaban kasar ya kaddamar.
Manufar shirin ita ce magance matsalar rashin aiki a tsakanin al’uma da kuma karfafa gwiwar ‘yan kasa su kasance masu dogaro da kansu.
Daga bisani mataimakin shugaban na Najeriya ya kaddamar da shirin gwamnatin jihar Kano na tallafawa matuka baburan Adaidaita sahu da kuma masu sana’ar likin taya domin inganta sanar’ar su.