Jerin laifuka 6 ne ake tuhumar tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, da tsohon ministan lamuran ketare, Aminu Bashir Wali da kuma Mansur Ahmed, tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano zamanin gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta farko.
Laiffukan 6 sun shafi yadda aka sarrafa Naira miliyan 950 da Jam’iyyar PDP ta fitar domin gudanar da yakin neman zabe a shekara ta 2015.
Haka kuma hukumar ta EFCC na tuhumar Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da karbar Naira miliyan 25 kowannesu daga cikin kudaden, yayin da hukumar ke tuhumar Injiniya Mansur Ahmed da amfana da naira miliyan 10.
Baya ga haka, dukkanin su akwai laifin sun yi tarayya wajen halatta kudin haram da kuma sarrafasu.
Bayan tafka mahawara tsakanin layoyin bangarorin biyu, a karshe kotun karkashin jagorancin Mai shari'a Zainab Abubakar, ta ba da belin mutanen uku bisa sharrudan cewa kowannen su ya kawo mai tsaya masa ma’aikacin gwamnati a matakin tarayya ko jihar Kano wanda bai gaza mukamin darakta ba.
Baya ga haka kuma, tilas ne ya mallaki gida ko fili a Jihar Kano mai dauke da cikakkun takardun gwamnati.
Haka zalika, kotun ta umurci masu belin su biyan naira miliyan 100 akan kowane guda daga cikin wadanda ake tuhuma, a duk lokacin daya tsallake beli.
Sannan su mika takardunsu na tafiya kasashen ketare.
Yanzu haka dai makusanta da magoya bayan wadanda ake tuhumar na alakanta wannan mataki na hukumar EFCC da sha’ani irin na siyasa.
Saurara cikakken rohoton Mahmud Kwari:
Facebook Forum