Rundunan sojin kasar a wata sanarwa da ta fitar , ta bayyana cewa ta samu nasarar tarwatsa tungar yan ina da kisa baya ga cafke wasu makiyaya dauke da makamai a jihohin Nasarawa, Binuwai da kuma jihar Taraba bisa zargin cewa suna shirin Kai hari .
To sai dai kuma, yayin da rundunar ke wannan ikirarin, wasu al'ummomi a yankin Wukari na jihar Taraba kokawa suka yi da harin da suke zargin sojoji sun kai musu da sunan yaki da bata gari.
Al'umman Chinkai sun yi zargin cewa an kai musu hari ba tare da wani dalili ba.
Duk kokarin da wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya yi, na ji daga bakin daraktan yada labaran rundunan soji a Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ci tura. An buga wayarsa to amma ba'a dauka ba, haka nan babu amsar sakon kar ta kwanan da aka aike masa.
To sai dai kuma shugaban karamar hukumar Wukari Hon Adi Daniel Adigrace ya bayyana abun da ya sani, a matsayinsa na babban jami'in tsaron yakin inda yace sojojin sun kai hari ne a mabuyan wasu yan ina da kisa na makiyaya.
Sojin sun yi bata kashi da makiyayan wadanda suka kona motocin sojoji biyu tare da haddasa rasuwar soji daya. Sauran sojojin ta kare suka yi kafin a kawo masu doki. Baicin sojan da ya mutu rikicin ya rutsa da ran wani farar hula kana wani kuma ya jikata.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Facebook Forum