Obasanjo ya bayyana cewa rashin fahimtar lamarin ne ya sa Buhari yin tuhumar.
Buhari ya yi gugar zanar ne a lokacin taron da kungiya magoya bayansa karkashin Kanar Hameed Ali mai ritaya inda ya ce "wani shugaba ko tsohuwar gwamnati ta kashe dala biliyan 16 kan wutar lantarki amma ba ga wutar ba."
Wannan ba yana nufin Shugaban na shirin binciken Obasanjo ba ne ba amma komai na iya faruwa idan aka yi la'akkari da yadda ya dage wajen caccakar gwamnatin Buhari da nuna cewa ta gaza.
Magoya bayan shugaba Buhari sun bayyana dalilin da ya sa suke tarurruka na musamman domin mayarwa shi Obasanjo martani.
"Babban matsalarsa ita kishi, ba ya son ganin duk wani mutum dan Najeriya ko da sunansa Buhari ko ma sunansa waye ne da ya samu wasu nasarori na ci gaban kasar nan, ya zama kishiya a gare shi." inji wani mai goyon bayan Buhari, Tasiu Muhammad Ringim.
Tasiu Muhammad ya yi tsokaci game da batun marawa Buhari baya a lokacin zaben 2015 inda har shi Obasanjo ya yaga katinsa na jam'iyyar PDP, da cewa lokaci ne ya yi da 'yan Najeriya su kudiri aniyar cewa sai an samu gyara akan makomar Najeriya, saboda haka, babu tabbacin tasirin matakin da ya dauka.
Yana ganin cewa babban jigon jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu shi ya kasance mutum mafi inganci a wannan lokacin daga yammacin Najeriya.
Saurari rohoton Nasiru El-Hikaya
Facebook Forum