Zazzabin Mura Ya Kama ‘Yan wasan Faransa

Mbappe

Kocin Faransa, Didier Deschamps, ya ce yana da kwarin gwiwa dukkansu za su samu sauki kafin wasan karshe da za su buga da Argentina.

Zazzabin mura ya ratsa cikin tawagar ‘yan wasan Faransa yayin da kungiyar take shirin karawa a wasan karshe na gasar kofin duniya.

A ranar Laraba Faransa ta doke Morocco da ci 2-0, za kuma ta hadu da Argentina wacce ta doke Croatia da ci 3-0 a wasan karshen.

Mai horar da ‘yan wasan na Faransa, Didier Deschamps, ya ce ‘yan wasa biyu sun nuna alamun cutar, wadanda suka hada da Dayot Upamecano da dan wasan tsakiya Adrien Rabiot.

Bayanai sun yi nuni da cewa an kuma killace su, lamarin da ya sa ba su buga wasan semi-final ba.

Rabiot dai ba ya cikin ‘yan wasan da suka kara a ranar Laraba a filin wasa na Al Bayt, shi kuma Upamecano na cikin jerin ‘yan wasan da aka tsara za su buga, amma ba a saka shi ba.

“Muna da sauran kwana hadu kafin wasanmu na gaba, saboda haka zai zama cikin shirin kafin ranar Lahadi.” In ji kocin na Faransa.

A cewar Deschamps, dan wasan gefe Kingsley Coman ma yana dan fama da zazzabi da ke nuna alamun murar ce.

Amma ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwar dukkansu za su samu sauki kafin wasan karshe da za su buga da Argentina.