Zazzabi Lasa: An Hallaka Beraye Dubu Hudu Da Dari Hudu A Kasuwanni 6

Ranar 25 ga wannan watan da muke ciki ne ofishin kula da lafiyar al'uma da ke jahar Legas ya fitar da sanarwar hallaka beraye har sama da dubu hudu da dari hudu a wasu kasuwanni guda shida dake wurare daban daban a fadin birnin a yunkurin da kungiyar ke yi na shawo kan zazzabin LASSA wanda bincike ya nuna cewar daga bera cutar ke komawa jikin dan' adam.

Shugaban kungiyar Mr Samuel Akingbehin ya bayyana wa mujallar New Nigeria cewar hukumar ta gudanar da ayyukanne a kasuwannin da suka hada da Onigongbo, da Oshodi, da Oke-Odo, da Ikotun Idanwo, da Ojuwoye da kuma kasuwar Mile 12.

Shugaban ya ce sun gudanar da ayyukanne domin rage yaduwar annobar cutar zazzabin Lassa mai saurin kisa a fadin jahar.

Daga lokacin da annobar ta barke, kawo yanzu ta hallaka mutane 76 da kuma kwantar da sama da jama'a 200 a jahohi 17 cikin talatin da shidda dake fadin kasar.

Yanzu haka dai hukumar ta ba jama'a damar cigaba da saye da sayarwa a kasuwannin kamar yadda suka saba.