Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bunsurun Soja! Dubban Sojoji Suka Halarci Bukin Yaye Shi A Ingila


Bunsurun Soja
Bunsurun Soja

Soja birgimar hankaka! Wannan shine kirarin da ake ma sojoji. Samun aikin soja ba karamin abu bane, a kowace rundunar sojoji ta kowace kasa a duniya. Fusilier Llywelyn, wani dan’akuya ne mai watani 10 da haihuwa, wanda akayi bukin yaye shi daga makarantar sojojin kasar Ingila. Kimanin mutane sama da 100 suka halarci bukin yaye wannan dan-tauren.

Bisaga al’ada, sojojin Ingila kan yi amfani da Bunsuru a yayin bukukuwan su wanda wannan yasamo asali tun shekaru 450 da suka wuce. A watan Mayu na shekarar da ta gabata wani Bunsuru mai matsayin Lutanan Kaftin Gwillam Taffy VI, ya mutu bayan nan kuma Sarauniyar Ingila ta bada umurnin a sake samo wani Bunsurun don ya maye gurbin wanda ya mutu. Shi dai Llywelyn, an yaye shi da mukamin Lutanant, kuma zai shiga rundunar Bataliyan ta 1, shine kuma soja mafi karancin shekaru.

Yanzu haka dai an fara yimishi shirye shirye don halartar bukin cikan Sarauniyar Ingila shekaru 90 da haihuwa, da za’ayi nan bada dadewa ba. An dai zabo shine bayan wata jarabawa da akayi musu tsakanin shi da wasu, an iya gane cewar shine yacan canci zama soja mai wannan mukamin, domin kuwa yanuna alamun yana da basira. A gaban goshin shi ana iya ganin mukamin shi.

Wasu daga cikin ayyukan shi a kullun, shine da safe zai yi atisaye da sauran abokan aikin shi mutane, kuma ya duba yadda tsaftar su take da lafiyar kowa. Abu mai matukar muhimanci, yana daya daga cikin mutanen da zasu dinga tsaron Sarauniyar Ingila a fadar ta ta Buckingham. Hakan na nuni da cewar hazakar shi ta kai hazaka, domin kuwa ba kowa ake kaiwa yayi aiki a gidan sarauniya ba, sai wanda aka sani yana da kwazo. An kuma ware mishi dakin shi da gadon shi kujerar shi da duk wani abu da ake sama soja a daki.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG