Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban San Motar Sata Bace - Inji Wani Limamin Coci


Wani limamin Cocin Presbyterian mai suna Rev Titus ya ce ya taka sawun barawo ne a yayin da jami'an 'yan sandan jahar Lagas dake Ikeja suka tasa keyar sa tare da wasu da ake zargi da aikata fashi da makami su biyar.

Mujallar Vanguard ta wallafa cewa malamin ya bayyanawa jami'an tsaron cewa mai sayar da motocin ya kawo masa kyautar motar ne ba tare da yasan cewa ta sata bace, daga cikin wadanda jami'an tsaron suka taso keyar su sun hada da wani matashi mai suna Opeyemi Aregbesola mai shekaru 28 da haihuwa, da Bola Salami mai shekaru 30, da Osas Felix mai shekaru 32, da Chibike Umeh mai shekaru 22, da kuma Ndibe Samuel mai shekaru 31.

Bayan kamun da jami'an suka yi ne aka gane cewa biyu daga cikin wadanda aka kama na cikin fitattun 'yan fashin da aka dade ana nema ruwa a jallo domin irin kaurin sunan da suka yi wayan aikata fashi da makami.

Opeyemi Aregbesola da Bola salami sun taba kwace wata mota Toyota Camry kirar 2007 mai lamba MUS782D.

A yayin da aka shigar da wadanda ake zargin harabar ofishin jami'an tsaron, kwamishinan 'yan sandan jahar Fatai Owoseni ya bayyana cewar a cikin binciken da aka gudanar akan matasan ya bayyana cewa sun dauki llokaci mai tsawo sun aikata irn wanna muguwar aika aika.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG