Babbar kotun tarayya ta Abuja ta bada belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a kan kudi Naira miliyan 500.
Mai Shari’a Emeka Nwite wanda ya jagoranci zaman kotun a yau Juma’a ya umarci tsohon gwamnan ya samar da mutane 2 da za su tsaya masa wadanda suma za su samar da Naira miliyan 500 kowanensu.
Haka kuma yace wajibi wadanda za su tsaya masan su mallaki filaye ko gidaje a Abuja.
Bugu da kari, sai mukaddashin magatakardan kotun ya tantance takardun kadarorin, wadanda wajibi ne su kasance a Abuja.
Mai Shari’a Nwite ya bada umarnin cewar wajibi ne tsohon gwamnan ya mika fasfo din tafiye-tafiyensa ga kotun, a yayin da shi da masu tsaya masa guda 2 zasu mikawa kotun kananan hotunansu na kwana-kwanan nan guda bibbiyu.
Haka kuma ya zaratar da cewa a ci gaba da ajiye Yahaya Bello a gidan gyaran hali na Kuje har sa’ilin da zai cika ka’idojin bada belinsa.
Yahaya Bello dai yaki ya amsa laifin zambar Naira biliyan 80 da hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ke tuhumarsa da aikatawa.