El Clasico: Zaratan ‘Yan Wasan Barcelona Da Ke Jinya Sun Fita Atisaye

'Yan wasan Barcelona lokacin da suke atisaye (Photo by Josep LAGO / AFP)

A ranar Asabar kungiyoyin biyu za su kara a karon farko a fafatawar hamayya a wannan kakar wasa.

Manyan ‘yan wasan Barcelona da ke fama da jinya sun fita atisaye, kwana gabanin karawar da kungiyar za ta yi da babbar abokiyar hamayyarta Real Madrid.

A ranar Asabar kungiyoyin biyu za su kara a karon farko a fafatawar hamayya a wannan kakar wasa.

Kusan wata guda Barcelona ta kwashe ba ta saka Robert Lewondowski da Frenkie de Jond, Pedri Gonzalez da Jules Kounde.

Dukkan ‘yan wasan na fama da rauni.

'Yan wasan Real Madrid suna atisaye. (Photo by OSCAR DEL POZO / AFP)

Sai dai dukkansu sun fita atisaye kwana guda gabanin haduwarsu da Real Madrid a karawar ta “clasico.”

Sai dai kocin Barcelona Xavi Hernandez bai ambaci ko day daga cikinsu zai buga wasan ba.

“Ba za mu yi kuskure mu saka wanda bai zama cikin shiri 100 bisa 100 ba.” In ji Hernendez.

Shi dai kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce ba shi da damuwa ko wa Barcelona za ta saka muddin dan wasansa Jude Bellingham zai buga.