Zanga-ZangaTa Zama Ajalin Wani Mutum A Kasar Senegal

Wani matashi ya mutu a birnin Kaolack cikin zanga-zangar neman yin waje da shugaba Abdoulaye wade.

Wani matashi ya mutu a Kaolack cikin zanga-zangar kin jinin shugaba Abdoulaye Wade

A kalla mutum daya ya mutu a kasar Senegal ana sauran mako daya zabe, lokacin da masu zanga-zanga su ka gwabza da da 'yan sanda a kan kokarin da shugaba Abdoulaye Wade ya ke yi ya sake tsayawa takarar neman wa'adin mulki na uku.

Jami'ai sun ce an kashe wani matashi ranar Lahadi a birnin Kaolack, mai kimanin tazarar kilomita 180 a kudu maso gabas da Dakar, babban birnin kasar. Masu zanga-zanga sun toshe tituna da dama a tsakiyar birnin Dakar, inda su ka yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu, su kuma su ka yi ta mayar da martani da barkonon tsohuwa da harsashan roba.

Shugaban kasar Senegal Abdoulaye Wade

Akwai rahotannin cewa mutane da yawa sun ji ciwo.

'Yan hamayya, da ke karkashin hadakar M23 sun ce Mr. Wade bai cancanci sake tsayawa takara ba saboda kundin tsarin mulkin kasar Senegal ya takaita shugabancin kasa ga wa'adin mulki biyu. Amma a watan jiya na Janairu kotun kolin kasar Senegal ta yanke hukuncin cewa dokar ba ta shafi Mr.Wade ba tun da ya na kan karagar mulki dokar ta fara aiki.

Ya zuwa yanzu dai mutane shida ne su ka rasa rayukan su cikin fadace-fadacen da ake gwabzawa tun da aka fara zanga-zanga bayan hukuncin da kotun ta yanke.

Masu zanga-zangar kin yarda shugaba Wade ya yi takarar neman wa'adin mulki na uku