Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kidaya Kuriun Zaben Shugaban Kasar Senegal Mai Sarkakkiya


Shugaba Abdoulaye Wade na kasar Senegal mai neman wa'adin mulki na uku, wanda hakan ya janyo takaddamar siyasa a kasar
Shugaba Abdoulaye Wade na kasar Senegal mai neman wa'adin mulki na uku, wanda hakan ya janyo takaddamar siyasa a kasar

Dan takarar jam'iyyar hamayya Macky Sall ya ce ba makawa sai an yi zagayen fitar da gwani

Ana ci gaba da kidaya kuri’un zaben shugaban kasar Senegal da aka yi ranar Lahadi.

‘Yan takarar jam’iyyun hamayya na kokarin babbake shugaba Abdoulaye Wade daga karagar mulki, wanda ya kufula dimbin ‘yan kasar Senegal saboda neman tsawaita mulkin da yayi shekaru goma sha biyu ya na yi a kasar ta yammacin Afirka.

Sakamakon farko, ba da yawun hukumar zabe ba ya nuna cewa su na biye da juna kut da kut, sannan Macky Sall, daya daga cikin manyan masu hamayya da Mr.Wade, ya fada ranar Litinin cewa ba makawa sai an yi zagaye na biyu, na fidda gwani. Amma har yanzu hukumar zaben kasar Senegal ba ta bayyana sakamako ko daya ba.

Kakakin Mr.Wade, Amadou Sall, ya shaidawa sashen Turancin Ingilishin Muryar Amurka cewa ya na kyautata zato shugaban zai sake cin zabe, kuma duka ‘yan kasar Senegal za su yarda da sakamakon.

Da aka nemi jin ta bakin shi game da yiwuwar yin zagayen fidda gwani idan aka rasa dan takarar da ya yi rinjaye, sai Amadou Sall, ya ce wannan kuma ya danganta da masu kada kuri’a.

Ranar Lahadi shugaba Wade ya sha ihu daga daruruwan mutane lokacin da ya kada kuri’ar shi a mazabar gidan shi.

‘Yan hamayya sun ce neman wa’adin mulki na ukun da shugaban ya ke yi, ya sabawa kundin tsarin mulki bayan gyaran da ya rattabawa hannu ya zama doka a shekarar 2001 wanda ya takaita shugabancin kasar ga wa’adi biyu. Amma kotun tsarin mulkin da shugaban ya kafa ta yanke hukunci a watan jiya cewa dokar gyaran ba ta shafi Mr.Wade ba saboda da ya na kan mulki ta fara aiki.

‘Yan takara goma sha uku ne su ka kalubalanci Abdoulaye Wade a zaben, a cikin su har da Macky Sall da Idrissa Seck wadanda dukan su biyu sun taba yin firai minista a karkashin mulkin shi.


XS
SM
MD
LG