Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya nemi da a kwantar da hankula a Senegal


Zanga-zanga a birnin Dakar
Zanga-zanga a birnin Dakar

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kiran da a kwantar da hankula a Senegal, inda ‘yan sandan kwantar da tarzoma su ka fafata da masu zanga-zangar neman kar Shugaba Abdoulaye Wade ya shiga takara a karo na uku.

A wata takardar jawabin da ya gabatar da yammacin jiya Talata, Mr. Ban ya bukaci da dukkannin bangarorin su daina tashin hankali su rungumi tafarkin zaman lafiya wajen warware takaddamar zabensu.

Dubban ‘yan Senegal ne, galibi matasa, sun kaddamar da abinda aka ayyana shi da nufin zama zanga-zangar lumana a jiya Talata a babban birnin kasar Dakar. To amman, zuwa wayewar gari, sai zanga-zangar ta zama ta tashin hankali ta yadda dalibai su ka yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu suna kuma kona tayu. ‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun mayar da martani.

Shaidu da hukumomi sun ce wani dalibi dan shekaru 30 da haihuwa ya rasu bayan da wata mota ta markade shi a yayin zanga-zangar. ‘Yan sanda sun karyata zargin cewa motarsu ce.

Masu zanga-zangar na sukar hukuncin da babbar Kotun kasar ta zartas a makon jiya da ya amince wa Shugaban kasar dan shekaru 85 ya nemi wa’adi na karo na uku. Wani tanajin Kundin Tsarin Mulkin Kasar ya iyakance wa’adin Shugaban kasa zuwa biyu kawai, to amman Mr. Wade ya kawo uzurin cewa sai da aka zabe shi kafin dokar ta fara aiki.

XS
SM
MD
LG