Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mugabe ya cika shekaru 88 da haihuwa; ya sha alwashin cigaba da zama bisa gadon mulki


Shugaba Robert Mugabe da tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro
Shugaba Robert Mugabe da tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro

Shugaban Zimbabuwai Robert Mugabe ya cika shekaru 88 da haihuwa a yau

Shugaban Zimbabuwai Robert Mugabe ya cika shekaru 88 da haihuwa a yau Talata, inda ya yi shelar cewa lafiyarsa lau kuma har yanzu bai da ranar sauka daga gadon mulki.

A wata hira da shi da aka yada ta kafar labaran gwamnati da daren Litini, Shugaban na Zimbabuwai ya ce ya na da cikakken koshin lafiya kuma bai ma fara tunanin yin ritaya ba, ya kara da cewa a shekarun da ya ke a yanzu ya na ma iya yin tafiya mai ‘yar tazara.

Ya kuma ce tilas ne a yi zabe a kasar, duk ko da rashin sabon kundin tsarin mulkin da aka tsai da shawarar samarwa bisa yarjajjeniyar da ta tanaji gwamnatin rikon kwaryar ta yanzu.

Shugaba Mugabe ya kasance bisa gadon mulki tun bayan da Zimbabuwai ta sami ‘yancin cin gashin kai daga kasar Burtaniya a cikin shekarar 1980.

Ya sami yabo a shekarun farko-farkon shugabancinsa, to amman a halin yanzu an mai da shi saniyar ware a Yammacin duniya, inda gwamnatocin kasashen ke zarginsa da yawan cin zarafin bil’adama da kuma yin lahani ga tattalin arzikin Zimbabuwai.

Mai magana da yawunsa ya karyata rahotannin da ke nuna cewa ana kan masa jinyar cutar daji a kasar Singapore, inda ya yi ta zuwa yau da yawa cikin shekarar da ta shige.

XS
SM
MD
LG