Kawo yanzu dai zanga-zangar ta ci gaba da bazuwa a biranen Britaniyan inda aka yi ta ganin yadda masu boren ke kone-kone suna balle shagunan a yayin da jami’an ‘yan sanda suka yi ta harba hayaki mai saka kwalla domin kwantar da tarzomar
Dakta Salim Abatcha dan Najeriya mazaunin birnin Manchester inda rikicin ya fi kamari ya ce shakka babu ana fuskantar barazana daga masu kyamar baki amma gwamnati na daukar matakin da ya dace
A dai farkon wannan makon ne, wasu masu ra’ayin rikau suka shirya zanga-zangar bisa zargin baki da hannu a kisan wasu yara mata uku a wani gidan rawa da ke yankin Southport, bakin suma dai sun shirya tasu zanga-zangar don nuna adawa da zanga-zangar kyamar baki, a lokuta da dama sai jami’an yan sanda sun yi da gaske don hana arangama a tsakanin bangarorin biyu
Kasashe kamar Najeriya da Malaysiya da Indonesiya da Hadaddiya Daular Larabawa sun gargadi al‘umominsu da su yi taka tsantsana a kasar a yayin da gwamnatin Australiya ke cewa zanga-zangar ta bude kafar aukuwar ayyukan ta’addanci…..Idowu Olayinka dan Najeriya ne da y ace, gargadin da gwamnatin Najeriyar ta yi yasa ya kara daukar matakin ganin rikicin bai ritsa da shi ba…y ace duk da cewa rikicin bai kai inda yake ba amma tuni ya kara daukar matakin kariya tun bayan da ya ji sanarwar gwamnatin Najeriyar ina dai kallo a talabijin yadda ake ta kone-konen motoci da shaguna..
Tuni dai Firaiminista Keir Starmer ya yi ma yan kasar jawabi yana mai cewa ko kadan gwamnatinsa ba za ta laminci duk wani yunkuri na haddasa kiyaya a kasar ba.
Saurari cikakken rahoton Ramatu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5