Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga Sun Kawo Karshen Mulkin Hasina A Bangladesh

Firaiministar Bangladesh, Sheikh Hasina
Firaiministar Bangladesh, Sheikh Hasina

Hotunan bidiyo sun nuna yadda dubban mutane suke ta bazama akan titunan Dhaka, babban birnin kasar suna nuna farin cikin saukar firaiministar wacce ta kwashe shekaru 15 tana mulkar kasar.

Firaiministar Bangladesh Sheikh Hasina ta yi murabus daga mukaminta a ranar Litinin ta kume fice daga kasar a cewar majiyoyi da dama.

Hakan na zuwa ne yayin da ake samun rahotannin mutuwar karin mutane a tarzomar da ta barke wacce tana daya daga cikin mafiya muni tun bayan gomman shekaru biyar da kafa kasar wacce ke kudancin Asiya.

A wani jawabi da ya yi ga kasar a kafar Talbijin, Shugaban sojojin kasar Janar Waka-Us- Zaman ya ce Hasina mai shekaru 76 ta arce daga kasar yana mai cewa za a kafa gwamnatin rikon kwarya.

Yadda masu zanga-zanga suka mamaye gidan Hasina da ke birnin Dhaka ranar 5 ga watan Agusta, 2024.
Yadda masu zanga-zanga suka mamaye gidan Hasina da ke birnin Dhaka ranar 5 ga watan Agusta, 2024.

Rahotanni kafafen yada labarai sun ce an fice da ita daga kasar cikin wani jirgi mai saukar ungulu wanda ya nufi jihar Yammacin Bengal da ke gbashin India.

Wasu rahotanni kuma sun ce jirgin ya nufi jihar Tripura ne da ke arewa maso gabashin India.

Kamfanin Dillancin Labrai na Reuters bai kai ga tabbatar da wadannan rahotani ba.

Hotunan bidiyo sun nuna yadda dubban mutane suke ta bazama akan titunan Dhaka, babban birnin kasar suna nuna farin cikin saukar firaiministar wacce ta kwashe shekaru 15 tana mulkar kasar.

Kasar ta Bangladesh ta tsunduma cikin yanayi na zanga-zanga ne wacce ta jirkice ta koma tarzoma a watan da ya gabata bayan da dalibai suka nemi da a soke tsarin nan da ke shata yadda ake raba aikin gwamnatin mai cike da takaddama.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG