WASINGTON —
Labari da dumi duminsa na tabbatar da cewa Shugaban kasar Nijer, Mohamed Bazoum ya yi wa gwamnatinsa garambawul dazun nan da rana, inda aka sauya wa ministoci 6 wuraren aiki, cikinsu har da Ministan cikin gida Alkache Alhada (Alkash Alhada).
Wakilinmu a Yawai, Suleiman Barma ya ce kwana guda kenan bayan da wasu masu zanga zanga suka datse wa ayarin motocin sojan Faransa hanya a garin Tera, saboda zarginsu da gaza magance matsalar tsaron da ta addabi yankin Sahel.
Hukumomi sun sanar cewa a kalla mutane biyu ne suka rasu, wasu kuma 18 suka ji munanan raunuka sakamakon wannan tarzoma da tuni hukumomi suka ce sun kaddamar da bincike domin gano gaskiyar abinda ya faru.