An samu tankiya a daren jiya Lahadi a Hong Kong ya yin da masu zanga zanga ke kara bazuwa a kan titunan birnin, kana suna bijirewa ‘yan sanda da suke jefa musu barkonon tsohuwa da albarusan roba a cikin sa’o’I da dama.
WASHINGTON, D.C. —
Ya yin da ake ci gaba da samun arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zanga, an harba wani nau’in iskar gas da aka taba amfani da shi a baya a matsayin mataki na karshe domin hana masu zanga zangar isa ofishin wakilin China inda aka lalata a makon da ya gabata.
Masu zanga zangar sun kwashe sa’o’I da dama suna neman su isa wurin, amma sun ja baya yayin da aka sakar musu hayaki mai sa hawaye.
Yawancin masu zanga zangar sun ce sun lashi takobi zasu ci gaba da bijirewa wannan gwamnati da ta kawo tsaiko ga jerin gwanonlumana dake jan hankali a kan kafa tsarin zabe ta hanyar demokaradiya da kuma nemankafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan yadda ‘yan sanda ke gudanar da ayyukansu.