Iran na ganin cewar bukatar hadin gwiwa da sojojin kasashen Turai don bada kariya ga tankunanta masu dauke da Man-Fetur, zuwa gabar tekun Gulf, wani abun koma bayane a gare ta.
“Mun samu labarin suna shirin tura sojojin kungiyar kasashen Turai, a yankin tekun na Gulf, wanda sako ne mai cike da rudani, kana da kaskanci wanda zai haifar da zaman doya da manja” a cewar wani mai magana da yawun gwamnati Ali Rabiel yau Lahadi ta kafar yada labaran gwamnati.
Akwai karin matsin lamba, tun bayan daukar wasu matakai da Iran tayi akan gabar tekun Hormuz, yanki mai matukar muhimmanci da jirage ke kai-komo, a bakin gabar tekun Iran.
A farkon wannan watan ne dai sojojin Iran su kai ta sauka daga jirgi mai saukar angulu da wasu kananan jiragen ruwa, inda suka kwace wani jirgin Mai dauke da Tutar Burtaniya mai suna Stena Impero.
Facebook Forum