A yau Laraba, Boris Johnson, zai kama aiki a matsayin sabon Firam Ministan Birtaniya.
Hakan, na nufin, zai maye gurbin Theresa May wacce ta yi murabus a hukumance, bayan da ta gaza samar da tsarin da Birtaniya za ta bi wajen shirin ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai ta EU.
Johnson, ya yi alkawarin hada kan al’ummar, kasar tare da cewa zai "ciyar da ita gaba," yayin da yake murnar sakamakon kuri’ar da aka kada na Jam'iyyar Conservative, inda ya kayar da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Jeremy Hunt, don zama sabon shugaban jam'iyyar.
Bisa al’ada, Sarauniyar Ingila, Elizabeth ta biyu ce za ta ayyana a hukumance, cewa Johnson, ya hau mukamin na firai minister, bayan lashe zaben da ya yi.
Facebook Forum