Wasu jerin hare-hare, sun girgiza Kabul babban birnin Afghanistan a jiya Alhamis, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 58, ciki harda da jamian tsaron Afghanistan, su 38. Shugaban majalisar manyan hafsoshin Amurka, ya gana da jami’an a Afghanistan.
Yayin da uku daga cikin bama-bamin sun auna Kabul ne babban birnin kasar.
Mai magana da yawun Ministan harkokin cikin gidan kasar, Nasrat Rahimi ya ce wani dan kunar bakin wake a kan babur ya afka wa wata bas a Kabul wacce ta ke dauke da ma’aikatan ma’aikatar man fetur din kasar yayin da suke kan hanyar zuwa wajen aiki da safiyar jiya Alhamis, inda nan take mutane 11 suka mutu, sannan kuma aka kara tada wasu bama bamai duk a waje daya.
Duk da cewa an saba ganin harin bam a Kabul a baya.Akasari yakan hallaka duk wadanda ke filin ansha kashe manema labarai. An kara tada wani bam din a mota a kan titin Jalalabad a Kabul sa’o’i biyu bayan harin farko da aka kai.
An nuna a gidan talabijin din kasar, jama’a firgice a asibiti suna neman yan uwansu.
Wasu rukunin yan ta’addan kasar ne suka dauka alhakin kai harin.
Facebook Forum