Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira kai-tsaye ga Amurkawa da su ci gaba da samar da kudaden tallafi a fadan da Ukraine da Isra’ila ke yi.
Da yammacin ranar Alhamis Biden ya yi wannan kira a wani jawabi da ya yi daga mashahurin ofishinsa na Oval Office, wanda ba kasafai yake jawabi daga wurin ba.
Shugabaan na Amurka ya kuma yi nuni da irin ta’asar da aka tafka a yake-yaken biyu (Isra’ila/Ukraine) yana mai cewa, duk da cewa rikicin daban-daban ne, amma suna da kamanceceniya iri daya.
“Dukkan su suna kokarin shafe tsarin mulkin dimokradiyya a makotansu.” In ji Biden.
Yayin da yake shan alwashin takawa dukkansu birki, Biden ya ce “tarihi ya nuna cewa idan ba a ladabtar da ‘yan ta’adda ko masu mulkin kama karya, za su iya kara haifar da rudani da mace-mace da barna.”
Biden ya ce, zai yi maza-maza ya aikawa Majalisar Dokoki karin kasafin kudi, wanda zai ba gwamnati dama ta aiwatar da wasu shirye-shirye da ba ta saba yi ba – wato samar da hanyoyin “tabbatar da tsaron Amurka da kawayenta.”
“Wannan abu ne da zai biya kudin sabulu ga fannin tsaron Amurka har ma wasu al’umomin da ke tafe su ci gajiya.”
Sai dai Biden bai ambaci adadin kudin da zai nema ba, amma wasu kafafen yada labarai sun ruwaito wasu jami’ai da suka nemi a sakaya sunayensu suna cewa kudin zai kai dala biliyan 100.
Biden ya bai wa masu sauraren jawabinsa tabbacin cewa, Amurka za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Isra’ila a matakan da take dauka na mayar da martani ga harin 7 ga watan Oktoba da mayakan Hamas suka kai mata, wanda ya halaka sama da mutum 1,400 suka kuma yi garkuwa da mutum 200.
Isra’ila dai ta mayar da martani da hare-haren sama, wadanda suka halaka sama da mutum 3,000 suka kuma raba sama da mutum miliyan daya da muhallansu a Gaza, mafi akasarinsu Falasdinawa Larabawa.
Biden dai ya kara nanata sakonsa yayin ziyarar da ya kai a Tel Aviv, wacce ita ce ta farko da wani shugban Amurka ya kai a lokacin rikici a Isra’ila: inda ya ce, Amurka za ta tabbatar da karin ingancin dakarun Isra’ila kamar yadda ta saba yi cikin gomman shekarun da suka gabata.
“Za mu tabbata cewa makaran da ke dakile hare-hare na Iron Dome, sun ci gaba da kare sararin samaniyar Isra’ila,” kamar yadda aka dasa a shekarar 2011 don dakile harin rokoki.”
Dangane da Ukraine, Biden ya kuma nuna goyon baya ga tsaron kasar da cin gashi kanta da kuma makomar tsarin dimokridiyyarta.
“Idan muka zurawa Putin ido ya shafe ‘yancin gashin kan Ukraine, sauran masu ta da husuma a sassan duniya za su samu kwarin gwiwar kwaikwayonsa. In ji Biden.
“Rikice-rikice za su yadu a sauran sassan duniya, a yankin Indo Pacific da Gabas Ta Tsakiya.” Biden ya kara da cewa.
Shugaban na Amurka ya ce ya gana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a ranar Alhamis.
Shi dai wannan neman karin kudi da Biden zai yi na samun goyon bayan dukkan jam’iyyun siyasar Amurka a Majalisar Dattawa.
Amma dole sai an kai shi gaban Majalisar Wakilai, inda wasu mambobin majalisar suke kokwanton tura biliyoyin daloli don tallafa wa rikice-rikicen da ake yi kasashen waje, wadanda ba su da alamun karewa.
Wani abu da zai kara dagulawa Biden wannan buri nasa shi ne, Majalisar Wakilan da ‘yan Republican ke jagoranta, ta kwashe sama da mako biyu babu shugaba tun da ‘yan uwnsa ‘yan Republican suka tsige Kevin McCarthy.
Bisa doka, dole sai Majalisar ta zabi Kakaki kafin a amince da wata doka ko kuduri, ciki har da bukatar Biden yayin da har yanzu, babu dan Republican din da ya samu kuri’a 217 da ake bukata kafin zama Kakakin Majalisar ta Wakilai.