Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwar Kauyen Karakai

Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Gaggawa a Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kasuwar kauyen Karakai dake karamar hukumar Bundugu ta jihar Zamfara, inda suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama

Da yammacin jiya Alhamis ne ‘yan bindiga duka kai hari kasuwar kauyen Karakai, tare da harbin kan mai uwa dawabi. Jami’an ‘yan sandan yankin sun tabbatar da mutuwar mutane biyu, sun kuma ce wasu da yawa sun jikkata. Amma wasu rahotanni na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sun zarta hakan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da cewa ‘yan sandan dake sa ido a kasuwar basu iya tunkarar ‘yan bindigar ba akan lokaci.

Rahotanni sun nuna cewa an kwashe mutanen da suka raunata zuwa babban asibitin kwararru na Yariman Bakura dake Gusau, cikin mutanen da aka kai asibitin akwai masu dauke raunukan harbin bindiga.

A ranar Talatan da ta gabata ma wasu ‘yan bindigar sun kai wasu hare-hare a kauyukan Farin Zare da Orawa da kuma Sabon Gari dukkansu a gundumar gidan Goga dake yankin karamar hukumar Maradu a jihar Zamfara.

Kamar yadda al’umomin kauyukan ke cewa wannan harin yayi sanadiyar akalla mutane 30, duk da yake rundunar ‘yan sandan jihar ta ce mutane uku ne suka rasa ransu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta baza jami’anta domin farauto ‘yan bindigar da suka kai hare-haren.

Jihar Zamfara na fama da hare-hare a ‘yan shekarun nan tare da rasa ‘daruruwan rayuka, baya ga satar Shanu da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, lamarin da ke fadada zuwa jihar Sokoto dake makwabtaka da jihar Zamfara.

Domin karin bayani saurari rahotan Murtala Faruk Sanyinna.

Your browser doesn’t support HTML5

Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwar Kauyen Karakai - 2'58"