A makon jiya ne babbar kotun da ke Gezawa, karkashin jagorancin mai shari'a Mohammed Yahaya ce ta bada wannan umarni, biyo bayan abin data kira bujirewa umarninta da shugaban hukumar yaki da rashawar ta Kano ya yi a lokuta dabam-dabam.
Kotun dai na neman Muhuyi Magaji ya bayyana a gabanta ne domin amsa wasu tambayoyi game da wata shari’a tsakanin hukumar da yake shugabanta da wata mata mai suna Hajiya Farida Tahir wadda hukumar ta yaki da rashawa ke tuhuma da yin sama da fadi da kudade.
Bayan aika sammaci har sau uku ga Muhuyi Magaji, kotun ta bai wa ofishin mataimakin sufeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya izinin ya kama tare da gurfanar da Muhuyi a gabanta a ranar 18 ga wannan wata na Yuli.
To amma, zaman da kotun ta yi a larabar nan 18 ga wata, hukumar ‘yan sanda ba ta kai ga cimma wancan umarni na kotu ba, hasali ma babu wani jami’in da ta tura domin yi wa kotu bayani game da halin da ake ciki.
“Gaskiya ne mun karbi umarnin kotu na kawoshi a gabanta, sai dai muna nan muna aiki akan umarnin har yanzu,” inji DSP Sambo Sokoto, Kakakin shiyya ta daya ta rundunar a nan Kano.
Kakakin ya bayyana cewa har yanzu ba su ganshi ba, amma sun samu bayanan cewa ya tafi kasar waje aiki amma da zarar suka gamu da shi za su kamo shi, sai in har kotun ta bayar da wani umarnin data shafe ta farkon.
Sa’o’i kalilan bayan umarnin kotu na aka kamo Muhuyi Magaji, shi kuma sai ya fitar da takardar ban hakuri da neman afuwa ga bangaren shari’a da sauran masu ruwa da tsaki dangane da rashin bayyanar sa a gaban kotun a can baya.
To ko hakan na nufin an samu fahimta kenan tsakaninsa da kotun wacce za ta kai ga janye wancan umarnin kamoshi?
"Babu abin da zai gotar da wannan umarnin sai a gaban kotu domin ba a janye irin wannan umarnin kawai a kasuwa ko kuma akan titi," inji Baba Jibo Ibrahim, wanda shine mai magana da yawun kotunan Kano.
Ya ce akwai matakan shari’a da ake bi domin janye umarnin kotu ba wai a bada hakuri kurum ba a ce shi kenan.
Yanzu haka dai kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Yuli, kuma a ranar ne ake sa ran ‘yan sanda zasu mika Muhuyi Magaji gaban kotu.
Facebook Forum