Shugabannin kungiyoyi daga shiyoyi hudu na kasar da suka hada da Ohanaeze Ndigbo, da Afenifere, da 'yan Niger-Delta da kuma dattawan Arewa suka yi zaman gano bakin zaren warware matsalar asarar rayuka da ke faruwa a kusan dukkanin jihohin Nigeria.
Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar Dattawan Arewa yace ba a da shugabannin siyasa na kirkiri a Nigeria. Farfesa Ango Abdullahi yayi wannan furucin ne wajen taron dattawan Nigeria domin gano hanyoyin magance yawan kashe kashe da satar mutane a Nigeria.
Haka kuma ya bayyana fatar sauran shugabannin jama’a za su bada nasu gudunmawa a wannan yunkuri da suka fara domin tabbatar 'yan siyasa sun yi abin da ya kamata. Ya ce hakan zai tilasta musu yin ayyuka "wanda zasu rage mana fitinun da muke ciki."
Shi kuwa Sanata Paul Wampana ya ce su kansu dattawan suna da nasu laifi a saboda haka ya kamata su binciki zukatansu. Yace su yin kurakurai. Kuskuren kuwa shine yin watsi da darasin da mutane irin su marigayi Sir Ahmadu Bello suka koyawa jama’a. A saboda haka yace dole a waiwayi inda aka kauce hanya domin a dawo kan hanya madaidaiciya. Ya ci gaba da cewa, dole ne bangarori su kulla kawance kafin a yi nasara musamman a harkar siyasar Najeriya.
Ya ci gaba da bada misalai, "Sardauna shi kansa in yaci zabe a arewa sai ya je neman hadin kan mutanen kudu maso gabas sannan a yi gwamnati. Haka ma a zamanin mulkin tsohon shugaba Shagari , ya ce bayan da suka ci zabe a Arewa, "sai da muka je muka nemi hadin kan yan kudancin Nigeria."
Wakilin kungiyar Inyamurai Ohanaeze Ndigbo, Dakta John Nwodo ya ce tun da suka yarda da juna har suka zo taron, dole ne su nemi mafita.
"Abubuwan da ke faruwa, wata dama ce ga kasarmu ta dakata don ta sake yin nazari," inji Nwodo.
Shi ma wakilin yankin Niger-Delta, Dattijo Edwin Clark ya ce a hada kai a kuma tashi tsaye.
"Idan aka zauna kawai ana kallon juna ba tare da an dauki kwararran matakai ba, to 'ya'yanmu ba za su taba yafe mana ba," inji Clark.
Kwararre a fannin zamantakewa, Dakta Sa'idu Dukawa ya ce a daina dora laifi akan shugabanni kadai. Yace Haduwar kanta muhimmiya ce, kuma har sai sanda aka samu wani abu mai kama da haka za a samu mafita.
Ya ci gaba da cewa, "Amma yadda haduwar da dauko turba ba lallai ta bulle ba, domin ga dukkan alamu duk bayanan da ake, ana tattarawa gwamnati ita kadai. Alhali kuwa yace akwai daidaikunsu, su 'yan siyasa har da wadanda suka zo taron nan, wadanda suke bata al'amura saboda burinsu na siyasa suke goyon bayan ta'addancin da ake yi."
Dukawa kuma ya yi gargadin illolin bangaranci da son zuciya a harkokin siyasa, inda ya ce, "idan ba a zo an daina wannan bangarancin da kuma son zuciyan na siyasa ba, duk inda ka kai ga dorawa gwamnati laifi ba za ta iya ba ita kadai."
Manyan dai sun ce za su zagaya kasar domin yin mubayi'a da sarakuna domin samun goyon bayansu wajen hadin kan kasa.
Facebook Forum