A wajen wani taron manema labarai a Yola,babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta nuna bacin ranta game da cin bashin da gwamnatin jihar tayi, baya ga kudaden tallafin da gwamnatin tarayya ta bada, batun da suka danganta da yunkurin jinginar da jihar Adamawa ta hanyar cin bashi.
Hon. Abdullahi Prembe, tsohon kwamishinan yada labarai dake zama sakataren jam’iyar PDP a jihar ya ce abun takaici ne ace yanzu bashin da ake bin jihar Adamawa ya rubanya na shekarar 2015, watau naira biliyan talatin da dori- zuwa sama da naira biliyan sittin a cikin shekaru uku kacal da gwamnatin APC ta yi a jihar.
"Gwamnatin PDP ta yi mulkin jihar na tsawon shekaru 16, basussuka da ta ci bai wuce biliyan 30 da wani abu ba. Amma yanzu maganar da na ke maka, an ci bashi sama da biliyan 30 a kasa da shekaru 4."
Ya bayyana akwai damuwa idan har aka ci gaba da haka wanda a cewarsa, jihar zata gurgunce ba ci gaba.
"Dole ire-iren wadannan abubuwa mu fito mu gayawa duniya saboda a samu mafita," inji Prembe.
Kamar dai yan PDP, suma yan bangaren integrity na jam’iyar APC da ke mulkin jihar sun nuna bacin ransu game da wadannan basussukan da ake zargin gwamnatin jihar ta ciwo a shekaru uku.
Kakakin 'yan Integrity Mallam Aminu Abdullahi Gambo Guyuk, ya ce duk da cewa jam’iyarsu ke mulki to amma kuma akwai bukatar sanin yadda gwamnati ke ciyo bashi da kuma yadda take kashe kudaden jihar domin 'yan kasa su sani.
To sai dai a martanin da gwamnatin jihar ta maida ta bakin kwamishinan yada labaran jihar Adamawan, Ahmad Sajo, ta yi fatali da wadannan zarge-zargen da yan jam’iyar adawa da kuma na Integrity group na jam’iyar APC ke yi.
"Ba mu ci bashi a wajen kowa ba, ba mu cin bashi. Dubara ce muka fitar ta tabbatar da mun yi ayyukan mu. Dubara ce wanda ya kamata a ce kowace gwamnati in ta samu kanta a yanayin da muke ciki, ta dauki wannan dubarar.
Game da batun nawa ake bin jihar, ko nawa aka samu a lokacin da suka karbi mulki? Sajo ya ce ba shi da masaniya tun da ba shine kwamishinan kudi ba.
"Idan na ce zan gaya maka, na yi karya," inji Sajo. Ya kara da cewa, "Ni dai na sani cewa a lokaci da muka karbi gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu, hatta albashin wannan ba a biya."
Wannan cece-kucen dai na zuwa ne a kasa da watanni biyar tun sadda Shugaba Muhammadu Buhari ya zo jihar Adamawan don bude taron yaki da cin hanci da rashawa.
Saurari rohoton
Facebook Forum