Harin ya haifar da kafa wani sansanin ‘yan gudun hijira na gaggawa a sakatariyar karamar hukuma Mulki ta Anka, domin tsugunnar da jama’ar garuruwan biyu mafi aksari mata da kananan yara.
Wakilin Muryar Amurka, Murtala Faruk, ya ziyarci sansanin, inda ya tarar da mafi akasarin mutanen dake gurin matane da kananan yara, wata daga cikin matan ta ce an kashe mijinta da kannenta guda uku.
Wata da ke magana cikin kuka da yanayin ban tausayi, ta ce mazansu sun tafi dauko gawarwakin mutanen da aka kashe, ashe ‘yan bindigar sun yi kwantan-bauna, inda suka afka musu da harbi suka kashe su.
A wani taron manema labarai, masarautar Anka, ta yi Allah wadai da harin tana mai cewa lamarin ya wuce nazarinta.
Wazirin Anka Muhammadu Inuwa, ya ce kan wannan abu da ya faru sun ayyana kwanaki uku domin zaman makoki, kuma za su yi azumi na kwanaki uku domin fadawa Allah halin da suke ciki.
Kan batun sojojin da aka aiki domin samar da zaman lafiya a yankin, Wazirin Anka ya ce duk lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin ana kiran sojojin amma kafin su je wajen an riga an gama barnar da za a yi.
Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin kashe duk wanda aka samu dauke da bindiga ba bisa ka’ida ba, sakamakon wani hari da ‘yan bindaga suka kai a kauyen Bawar Daji wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane fiye da talatin.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Murtala Faruk Sanyinna.
Your browser doesn’t support HTML5