Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Dake Yaki Da Fataucin Mutane, NAPTIN, Ta Ceto Yara 19


Yaran da aka ceto
Yaran da aka ceto

A wannan karon hukumar dake yaki da safarar mutane ta Najeriya ta samu nasarar ceto yara mata kananan su 19 dukansu ‘yan asalin Kano daga turasu gonar bauta a kasar Saudiya da sunan samar masu ayyukan yi

Jami’in hukumar dake yaki da fataucin mutane Mr. Josiah Emeron ya yiwa Muryar Amurka karin bayani akan ceto wasu.

‘Yan mata 19 dukansu ‘yan asalin jihar Kano da ake kokarin safararsu zuwa Saudiya.

Inji Mr Emeron nasarar tasu ta biyo bayan wani bayanan sirri da suka samu ne akan yara kananan a lokacin da ake dab da jigilarsu su zuwa kasar Saudiya. Yace ana tura yaran ne da suna zasu je su yi aiki ne amma daga bisani kuma sai a mayar dasu bayi, su dinga aikin bauta.

Shugabar kare hakkin mata a Najeriya Dr. Saudatu Mahadi tace irin wannan balaguron nada manyan illoli guda uku. Illa ta daya itace muddin suka tsallake daga kasarsu sun shiga inda basu da daraja ke nan. Ta biyu itace wulakanci da ake nuna masu. Illa ta uku ita ce budewa ‘ya’ya mata wata hanyar kwadayi da zai sa su shiga yin wasu muggan halaye.

Masanin halayyar bil Adama Farfesa Muhammad Tukur Baba ya baiyana dalilin da ya sa ake irin wannan tafiyar. Ya ce kowa yana tsammanin idan ya bar inda yake zuwa wani wurin zai samu jin dadi.

Shugaban hukumar wayar da kawunan ‘yan Najeriya Dr. Garba Abari ya ce dole ne gwamnatocin tarayya da na jihohi da shugabannin addini su tashi tsaye su dakile matsalar. Yace, su a hukumance suna fadakar da jama’a akan illar safarar mutane tare da yin maganin talauci wanda ke sa mutane barin kasarsu .

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG