Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ce Ke Kan Gaba Wajen Aiwatar da Hukumcin Kisa a Afirka


Kungiyar Amnesty International
Kungiyar Amnesty International

Kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoto da ya nuna Najeriya ce kan gaba wajen aikwatar da hukuncin kisa a nahiyar Afirka yayinda kasashe 20 cikin Afirka sun daina yanke hukumcin kisa kana wasu karin guda biyu na dab da dakatar da yanke hukumcin a kasarsu

Rahoton da Amnesty International ta fitar ya nuna Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen zartas da hukumcin kisa.

Kungiyar ta yabawa sauran kasashen Afirka, musamman kasar Guinea wadda ta kasance ta ishirin wajen kawo karshen yanke hukumcin kisa.

Kasar Kenya ta bi sawun kawar da hukumcin kisa a kasarta. Kasashen Burkina Faso da Chadi na daukan matakan da zasu kai ga daina yanke hukumcin kisa a kasashensu.

Alhaji Musa Jika daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar Amnesty International a Najeriya yace rahoton ya nuna cewa ya kamata alkalan kasashe irinsu Najeriya da gwamnati su dinga kula da yanayin shari’a a kasarsu. Yace barazanar hukumcin kisa ba zai magance wasu matsaloli ba, gara ma a ce an yake wa mutum hukumcin daurin rai da rai.

Rahoton dai ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo karshen hukumcin kisa a kasar. Matakin yin hakan ya dogara ne ga majalisun dokokin kasar. Alhaji Musa Jika y ace wajibi ne da yake rataye akan ‘yan majalisa su yi dokar kawar da hukumcin kisa.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG