Bayan da shugaban Najeriya ya fito ya bayyana anniyarsa ta sake tsayawa takarar zaben shugaban kasa na badi, wasu ‘yan jam’iyyarsa dake jihar Neja sun koka da abun da suka kira watsin da aka yi dasu.
Wadan nan ‘yan jam’iyyar da yanzu suka yi zugum har sun kafa wata kungiyar wadanda aka yi watsi dasu da ake cewa “Abandoned APC Members’ Forum” da turanci
Su dai wadan nan mutanen sun bayyana dalilinsu na jan dagan. Alhaji Muhammad Abubakar Kaca sugaban kungiyar y ace su ne suka yi fafutikar neman zabe har aka ci aka kafa gwamnati a tarayya da jiha. A cewarsa wadanda suka zo suka kafa gwamnati wadanda basu yi wahala ba ne. Su da suka yi wahalan sai aka turasu gefe daya.
Amma jigon jam’iyyar APC din a jihar Neja Abdulkadir Shehu Nafuntuwa y ace suna baiwa ‘ay’yan nasu hakuri. Yana kiransu su dawo a yi tafiya tare saboda mota bata barsu bay aba.
Masu korafin na cewa fatansu shi ne gwamnati ta inganta rayuwar mutanen karkara kamar yadda Alhaji Muhammad Abubakar Kaca ya fada. Ya yi misali da baiwa mutanen karkara wutar lantarki.
Ita gwamnatin jihar ta ce tana kokarin inganta rayuwar mutanen karkarar ta fannoni daban daban. Kwamishanan yada labaran jihar Alhaji Danjuma Sallau y ace sun dauki matakin gyara gandun dajin makiyaya dake kamfanin Bobi inda za’a gina makarantu da asibiti da hanyoyi da kasuwanni.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum