Zai yi Wuya Hukumar Zabe ta Hana Jam'iyyar Gwamnati yin Amfani da Kudi

INEC

Jam'iyyun hamayya da sauran jama’a na da damar kai korafin su kotu duk lokacin da aka karya wata doka.

Bisa ga tsarin hukumar zaben Najeriya, bai kamata ‘yan takara su yi amfani da kudi ko kayan aikin gwamnati wajen yin kamfe ba. Amma ganin halin da kasar ke ciki ko yaya hakan zai yiwu?

Shugaban Cibiyar harkokin demokradiyya na kasa-da-kasa Dr. Abbati Bako, yayi fashin baki a wata hira da yayi da sashen hausa na muryar Amurka inda ya ce, in har hukumar zabe zata kiyaye wadannan dokokin, to tabbas abu ne mai yiwuwa. Akwai shikashikan demokradiyya guda 35 a Najeriya, amma tun da aka fara mulkin demokradiyya a kasar daga aluf dari tara da cisi’in da tara, babu dokar da ba a karya ba inji Dr. Bako.

Ya cigaba da cewa zai yi wuya hukumar zabe ta hana jam’iyyu musamman jam’iyar gwamnati yin amfani da kayan gwamnati da kuma kudade wajen yakin neman zabe.

Dr. abbati ya kara da cewa idan har za a bi demokradiyyar gaskiya, jam'iyyun hamayya da sauran jama’a na da damar kai korafin su kotu duk lokacin da aka karya wata doka wanda kuma in har aka zartar da hukunci cikin sauri, hakan zai iya takama ‘yan siyasa burki.

Your browser doesn’t support HTML5

Zai yi Wuya Hukumar Zabe ta Hana Jam'iyyar Gwamnati yin Amfani da Kudi - 3'08"