Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Zasu Yi Anfani da Kowace Kafa Su Ci Zabe-inji Jonathan


Shugaba Jonathan
Shugaba Jonathan

Yayin da yake fafitikar neman kuri'a shugaba Jonathan ya ce 'yan adawa zasu yi anfani da kowace kafa su ci zabe.

Zasu yi anfani da tsorataswa, kage da yin anfani da kafafen labarai 'yan gaza gani da sauransu.

Shugaba Jonathan ya gargadi masu saurarensa kada su bi 'yan adawa. Jonathan yace abu ne mai karfafa kwarin gwiwa yadda alamuran tsaro suka dan inganta. Kuma idan Allah ya yadda za'a yi zabe a duka jihohin Najeriya.

Ita ma uwargidan shugaba Jonathan Dame ta fito karara ta soki kalamun da aka alakanta da Janaral Buhari inda yace idan ya ci zabe zai soke ofishin matar shugaban kasa. Tace ba zasu zabi duk wani shugaba da yake son ya mayar dasu kicin domin dafa abinci ba. Sabili da haka ta kira kowa ya marawa shugaba Jonathan baya.

Su ma magoya bayan neman canji irinsu Sanata Danjuma Goje sana ganin jam'iyya mai mulki ke da halin razanarwa ko takurawa adawa. Ya roki mutane irin su gwamna Sule Lamido su duba halin da arewa ke ciki su marawa Janaral Buhari baya domin ya ceto yankin daga wahalar da ya shiga. Yana cewa idan Sule Lamido ba zai fito ya goyi bayan Janaral Buhari ba to kada ya batashi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

XS
SM
MD
LG