Hakan dai na zuwa a dai-dai lokacin da shi Adamu Mainan ya yi taron kaddamar da yakin neman zabensa a Dutse Jihar Jigawa.
“Adamu ba zai ci ba, kuma ba zai bari a ci don rashin gaskiya ba. Adamu zai muku aiki”, a cewar Sanata Lawal Girgir, mataimakin shugaban PDP na kasa dake kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, a lokacin da ake taron kaddamar da yakin neman zaben Adamu Maina Waziri a birnin Dutse, fadar gwamnatin Jihar Jigawa.
Shettima Muhammed Saleh shine Darakata Janar na kwamitin yakin neman zaben na Adamu Maina.
“Wadannan jama’a da ka gani, jama’a ne dake wakiltar bangare-bangare daban-daban na PDP wadanda aka yi taro da su, a Kaduna, wanda mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo ya jagoranta”.
Rigingimun da suka biyo bayan zaben fidda gwani na dan takarar gwamnan Jihar Yobe ne yasa aka gudanar da wannan taro.
Sai dai lamarin daya dauki hankulan Jama’a shine an gudanar da wannan yakin neman zabe ne a Jihar Jigawa, ba Jihar Yobe ba inda dan takarar yake sha’awar shugabanta.
Adamu Maina Waziri cewa yayi “ina so ince na sake zama dan takara, don har yanzu ban cimma burina ba, na neman shugabancin Jihar Yobe, don in kawo shugabanci na gari.”
Sai dai Ambasada Umar Iliya Damagun wanda jigo ne a PDPn Jihar Yobe cewa yayi “ina so na jawo hankalinmu gaba daya, shi mulki na Allah ne. Kuma shi yake bayarwa a lokacin da yaga dama. Tunda Allah Ya baiwa mutum guda, yanzu dole ne mu jajirce, mun dunkule mu cure”.