Dr Abdullahi Ganduje yanzu shi ne mataimakin gwamnan jihar ta Kano kuma dan kwankwasiya ne.
Sauran jam'iyyun kamar su ANPP da ACN da CPC da dai sauransu suna zaton za'a fitar da mataimakin gwamna ne daga cikinsu, to amma a karshen makon jiya sai aka sanarda sunan Dr Habiz Abubakar wanda shi ma na hannun daman gwamna Rabiu Kwankwaso ne, wato shi ma kwankwasiya ne, a matsayin dan takarar mataimakin gwamna.
Wannan hukuncin na APC ya harzuka magoya bayan Abdulrahaman Kawu Sama'ila daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar gwamnan Kano kuma dan asalin ANPP.
Wani dake fafitikar neman an zabi Janaral Buhari yace Kawu Sama'ila ne kawai a Kano yake taimaka masu da zaben Buhari. Idan har ba za'a ba shi mataimakin gwamna ba a Kano to ko zasu tarwatsa duk zabukan Kano APC tayi asarar Kano gaba daya. Wani yace watan faduwar APC a jihar Kano ya kama.
Malam Musa Gwadabe daya daga cikin dattawan APC yace a hakura kada a ce za'a bar jam'iyyar. Abu mai wucewa ne.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.