Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga shugaba Goodluck Jonathan cewa ya yi watsi da wani abun da ke sanya shi zullumin wani abu zai same shi idan ya bari ya fadi zaben.
Da ya juya kan Janar Buhari sai ya ce ya kawar da fargaban da wasu ke yi cewa zai dauresu idan Allah ya bashi zaben.
Wadannan abubuwa dai suna cikin dabarun da 'yan siyasa daga bangarorin biyu suke amfani da su da nufin hakan zai baiwa takararsu nasara.
Musa Sarkin Adar na APC ya ce wata dabara ce aka fito da ita da nufin batar da hankalin jama'a.
Wasu ne ba sa son wata jam'iyya ko wani dan takara su na amfani da hikima su kawar da hankalin mutane.
Ya ce cancanta na da kyau amma mutane su yi tunanen zaben shugaban da zai taimakesu ya biya masu bukatunsu.
A wasu jihohin arewa wasu suna tunanen zabar gwamnoninsu amma a zaben shugaban kasa su yi adawa. Misali a Gombe jama'a suna fada zasu zabi gwamnansu Dankwambo amma a matsayin shugaban kasa zasu zabi Janar Buhari.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5