Hedikwatar 'yan sandan Najeriya za ta tura manyan Mataimakan Sufeton 'Yan sanda Biyu da kuma karin kwamishinonin 'yansanda takwas don samar da tsaro yayin zaben gwamna da za ai a jihar Edo.
Kakakin Rundunar Yanssndan Najeriya, DCP Frank Mba ya fada cikin wani sako da ya aike wa Muryar Amurka cewa wadannan manyan hafsoshin Yan sandan za su tabbatar da bin ka'idoji da dokokin zabe yayin gudanar da zaben wanda za ai a makon gobe.
Rundunar yansandan ta tabbatar da cew za ta yi aiki tukuru don ganin an bi doka da oda yayin wannan Zabe.
A cewar masanin kimiyyar siyasa, Dakta Abubakar Umar Kari, kodayake wannan ba wani sabon abu ba ne amma da kyar in har hakan zai hana tayar da hankali.
A cewar masanin, abin da zai hana tada hankali shi ne, su mutanen jihar su kasance masu son zaman lafiyar.
Su kuwa yan kungiyoyin fararen hula irinsu Comrade Abubakar Abdulsalam na ganin kuskuren tura jami'an tsaro masu yawa haka hidindimu na siyasa, alhalin kuwa 'yan bindiga da 'yan Boko haram na can na cin karensu ba babbaka.
Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5