A cewar jama'a musamman ma a shafukan sada zumunta, "inda sun yi la’akari da yadda al’ummar kasar ke fama da kuncin rayuwa ba za su yi haka ba."
Wasu kuma sun yi ta sukarsu sakamakon yin biki a lokacin da aka gindaya dokoki wadanda suka haramta cunkoson jama'a.
Bikin auren Aisha Hanan Muhammadu Buhari da angonta Muhammad Turab Sha’abab, ya zo ne a dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke korafin hauhawa da kuma kari a farashin kayakin masarufi, man fetir da kuma kari a kudin wutar lantarki a kasar.
Dan fafutuka kuma shugaban wata kungiya dake rajin bin diddigin kuddaden da aka yi sama da fadi da su a kasar, Hamzat Lawal ya ce bai kamata iyalen farko a Najeriya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari su yi irin wannan biki a cikin yanayi da kasar ke fama da annobar Cutar Covid19 ba. Wadda ta yi sanadiyar rasa aikin yi ga matasa da kaso 55 cikin 100 cikin watanni 3 zuwa 5.
Hukumar 'yan sanda dai ta sha kai samame da kama masu sayar da sabbin kudaden takarda na kasar don liki a wuraren biki, mai fashin baki akan al’amuran yau da kullum a Najeriya, Malam Zakari Lamba ya ce a wannan karan hukumar 'yan sanda ta yi sakaci wajen yin aiki yanda ya kamata.
Saba wa Dokar Babban Bankin Najeriya ta shekarar 2007 Sashi na 21 ne, da ke nuni da cewar a hukunta wanda aka kama da laifin watsa kudin kasar ta hanyar yin liki, ko zaman kaso har na tsawon watanni 6, ko biyan kudin beli Naira dubu 50.
Amma dai masanin shari’a Barista Umar Mainasara Kogo ya ce rashin bin doka da manyan masu mukamai a kasar ke yi shi ke mayar da hannun agogo baya.
Ga Shamsiyya Hamza Ibrahim da cikakken rahoton:
Facebook Forum