Lamarin ya yi sanadiyar arcewar mutanen dake karamar hukumar zuwa sansanonin 'yan gudun hijira dake wasu garuruwan da ayyuakn ‘yan ta’adda ke da sauki amma kuma yanzu suke cikin wani mawuyacin halin rayuwa.
An fara kai hari a karamar hukumar ne a shekarar 2014, inda aka kashe mutane da dama da jami’an tsaro kana aka kone dukkan gine ginen gwamnati dake garin, wanda hakan yasa mutanen gari kauracewa gidajen su baki daya.
Kakakin majalisar ya ce bayan hawan shugaba Muhammadu Buhari a kan karagar mulki a shekarar 2015, babban hafsin sojan kasa a Najeriya, Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai ya jagoranci wata runduna inda suka kwato garin na Guzamala daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
Kakakin majalisar, Abdulkareem Lawan, ya ce bayan watanni biyu zuwa uku kugiyar ta Boko Haram ta sake kai hari a karamar hukumar wanda hakan yasa mutane sake ficewa daga garin zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira har zuwa lokacin da aka sake yin wani zabe a shekarar 2019.
Ya kara da cewa “muna da garuruwa fiye da 185 a yankin, amma yanzu haka babu mutum koda guda a wurin. A dan haka ina kira ga gwamnatin tarayya ta kawo mana dauki ta maido da zaman lafiya a karamar hukumar Guzamala”.
Wasu mutanen karamar hukumar dake a sansanonin ‘yan dugun hijira da suka tattauna da Muryar Amurka sun bayyana irin wahala da suke sha dasu da ‘ya’yan su.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:
Facebook Forum