Zaben Amurka: Yadda Muhawarar JD Vance, Tim Walz Ta Kaya

J.D. Vance (Hagu) Tim Walz (Dama) a muhawarar da suka yi a birnin New York

Abokan takarar biyu sun amince cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke cikin Amurka ba bisa ka’ida ba babbar matsala ce.

Mataimakan 'yan takarar mataimakin shugaban kasa JD Vance da Tim Walz sun yi amfani da lokacin su a dandalin muhawarar wajen mai da hankali kan yawancin hare-haren su, ba kan junan su ba, amma kan wadanda ke kan gaba a takardun 'yan takarar abokan hamayyar su.

Vance na jam’iyyar Republican da Walz na jam’iyyar Democrat duka sun yi kokarin nuna kansu a matsayin abokan hamayya masu saukin kai yayin da suke suka ga Harris da Trump.

Tare da rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya, mataimakan 'yan takarar shugaban kasar biyu sun bayar da hanyoyi daban-daban game da manufofin kasashen waje: Walz ya yi alkawarin "jagoranci mai daidaito" a karkashin Harris.

A gefe guda Vance ya yi alkawarin dawowa da "zaman lafiya" idan Trump ya dawo Fadar White House.

Abokan takarar biyu sun amince cewa yawan 'yan gudun hijirar da ke cikin Amurka ba bisa ka’ida ba babbar matsala ce.

Amma kowannen su ya jingina laifin kan dan takarar shugaban kasa na bangaren abokin hamayyarsa.

Muhawarar ta ranar Talata ta zo ne a lokacin da muhimmancin batutuwa ke faruwa a duniya inda Iran ta harba makamai kan Isra'ila.

Mataimakan 'yan takarar shugaban kasa sun yi musayar yawu kan tashin hankali a Gabas ta Tsakiya, sauyin yanayi da batun yin kaura.