Tim Walz da JD Vance zasu fuskanci juna a karon farko na mahawarar 'yan takarar mataimakin shugaban kasar Amurka gabanin zaben watan Nuwamba, kuma ana jin ita za ta zamo irinta daya tilo.
Walz da Vance zasu fafata ne a dandalin mahawara na birnin New York da yammacin yau Talata a yayin da yakin neman zabe ke shiga matakin karshe gabanin zaben da za'a yi cikin watan Nuwamba mai zuwa.
An zabi Walz, wanda ya kasance gwamnan jihar Minnesota, ya kasance abokin takarar 'yar takarar shugabanci Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Democrat, Kamala Harris a watan Agustan da ya gabata.
An kuma ayyana Vance, wanda ya kasance sanata daga jihar Ohio ya zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga dan takarar shugaban kasar jam'iyyar Republican, Donald Trump, a babban taronta daya gudana cikin watan Yulin da ya gabata.
Tun daga wannan lokaci 'yan takarar mataimakin shugaban Amurkan suka karade fadin kasar suna gudanar da gangami da tarurruka domin neman kuri'un masu zabe.
Mahawarar ta ranar Talata zata basu damar bayyana manufofin da zasu baiwa fifiko tare da baiwa jam'iyyunsu karin karfin gwiwa a zaben da ake yiwa kallon za'a fafata a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Dandalin Mu Tattauna