Sakamakon da aka sanar a ranar Lahadin da ta gabata, shi ne zabe mafi muni ga jam'iyyar ANC wacce ke da rinjaye tsawon shekaru 30 tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata, inda ta kasa samun yawan kujeru a zaben majalisar dokokin kasar da ya gudana.
Jam’iyyar wadda Nelson Mandela ya taba jagoranta ta lashe kujeru 159 ne kacal cikin 400 inda a baya ta samu kujeru 230.
Zaben ya kafa tarihi, inda jam'iyyu 70 da kuma 'yan takara masu zaman kansu 11 suka fafata domin neman kujerar majalisar dokoki da kuma ta lardi.
Sakamakon da aka sanar a ranar Lahadi na nuna yadda farin jinin jam’iyyar ke dusashewa, kuma hakan na nufin wajibi ne a yanzu jam’iyyar ta shiga kawance domin kafa gwamnati mai zuwa.
Jam'iyyar ANC ta rasa goyon bayan jama'a ne saboda karuwar rashawa da laifuka da kuma rashin aikin yi.
A yanzu dai jam’iyar ta tabbatar da aniyar ta na fara tattaunawa da wasu jam'iyyun siyasa da nufin kulla kawance da za ya bayar da dama na kafa gwamnatin hadin gwiwa.
Sakatare Janar na jam'iyyar ANC, Fikile Mbalula ya bayyana cewa, "jam’iyyar ta ANC ta kuduri aniyar kafa gwamnatin da za ta kare muradin al'ummar kasar, wadda ta tsaya tsayin daka kuma za ta iya gudanar da mulki yadda ya kamata."