Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN AFIRKA TA KUDU: Jam'iyyar ANC Na Iya Rasa Rinjaye A Majalisar Dokoki


Electoral Commission of South Africa (IEC) officials put up a sign outside a polling station in Umlazi on May 29, 2024 during South Africa’s general election.
Electoral Commission of South Africa (IEC) officials put up a sign outside a polling station in Umlazi on May 29, 2024 during South Africa’s general election.

'Yan Afirka ta Kudu sun fara jefa kuri'a a zaben da ake yi wa kallon mafi muhimmanci a kasar a cikin shekaru 30, kuma wanda ka iya daga martabar dimokraɗiyyar ƙasar zuwa wani matsayi.

Jam’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu na fafutuka a yau Laraba domin hasashen da ake yi na cewa za ta iya rasa madafun iko na tsawon kusan shekaru 30 da ta yi, a daidai lokacin da masu kada kuri’a suka fito babban zaben kasar.

Sama da masu kada kuri’a miliyan 27 ne suka yi rijistar zabar 'yan majalisar dokoki wadanda daga baya kuma za su zabi shugaban kasa.

APTOPIX South Africa Election
APTOPIX South Africa Election

Sai dai bayan kada kuri'a, Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda ke neman sake tsayawa takara, ya ce: "Ba ni da kokwanto a cikin zuciyata cewa, jama'a za su sake baiwa ANC kwarin gwiwar ci gaba da jagorantar kasar.

"Mutanen Afirka ta Kudu za su baiwa ANC gagarumin rinjaye."

Cyril Ramaphosa
Cyril Ramaphosa

Kasar da ta fi kowacce habakar tattalin arziki a Afirka ta fuskanci matsalar tattalin arziki da zamantakewa mafi muni a duniya, ciki har da rashin aikin yi da ya kai kashi 32 cikin 100.

Rashin daidaito wajen samun arziki da talauci da rashin ayyukan yi da ke shafar bakaken fata na barazanar kawar da ANC daga kan mulki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG