Zaben 2023: Tsohon Shugaba Jonathan Ya Gargadi 'Yan Siyasa Da Su Yi Ayyukan Su Da Tsafta

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari

Halin mu ‘yan siyasa yana da matukar muhimmanci ga sha’anin zabe, in ji tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yayin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kada kuri'arsa a jihar Bayelsa domin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar ranar Asabar.

“Kuma a koda yaushe ina gaya wa ‘yan siyasa cewa ‘Lallai, za ku iya cin zabe ta hanyar da ba ta dace ba, kamar amfani da tashin hankali wajen cin zabe ko sayen kuri’u da sauransu. Amma idan ka yi haka, kana zama kamar dan fashi da makami ko dan damfara ne, in ji shi.

Jonathan ya kara da cewa “Dan fashi da makami yana samun kudi ta hanyar fashi, amma kowa ya san shi dan fashi ne. Dan damfara yana samun kudi ta hanyar yaudarar mutane, amma kowa ya san cewa shi dan damfara ne. Ba su da mutunci tsakanin al'umma. "

A cewarsa, ya kamata ‘yan siyasa su kasance masu mutunci a cikin al’umma. Saboda haka, ya ce “dole ne mu gudanar da al’amuranmu cikin aminci” domin magoya baya, ‘yan uwa da sauran mutane za su amince cewa siyasa “ciniki ne mai tsafta.”

Ya bukaci ‘yan siyasa da su bar masu kada kuri’a su zabi shugabannin su a kowane mataki.

“Rokona shi ne, mu ’yan siyasa, jami’an tsaro, jami’an INEC su yi wa kasa aiki mai kyau saboda duk duniya tana kallonmu,” in ji shi.

“Dattawa da dama daga sassa na duniya suna cikin Najeriya saboda wadannan zabukan. Suna son mu yi nasara, kuma bai kamaci mu gaza ba.”

Jonathan ya yaba da tsarin tantance masu kada kuri’a (BVAS), inda ya bayyana tabbacin cewa duk da cewa ba za a iya kawar da ‘yan kura kurai ba, amfani da na’urar na nuni da irin ci gaban da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke yi.