Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Masu Kada Kuri’a Sun Nuna Damuwa Kan Rashin Ganin Sunayensu A Rumfunar Da Suka Saba Zabe


Wasu a layin kada kuri’a
Wasu a layin kada kuri’a

Tun farar safiyar yau Asabar da hukumar INEC ta tabbatar cewa za a gudanar da zaben shekarar 2023, a nan babban birnin tarayya Abuja mutane suka fito rumfunan zabe domin kada kuri’ar su.

A kokarin da hukumar zaben ta Najeriya INEC ta yi na rage cunkoson jama’a a runfunan zabe, ta kirkiri sabbin runfana saidai akwai wadanda suka fuskanci matsalar kasa gane rumfar zaben su, duk da cewa a wasu rumfunar an tanadar da motoci dake daukar mutane zuwa sabbin runfunan su.

Muryar Amurka ta halarci rumfar zabe dake Unguwar Mabushi a Abuja inda mu ka zanta da wasu mutanen da suka fito domin kada kuri’arsu inda suka bayyana cewa sun gudanar da zaben su lafiya matsalar wadanda basu gane rumfar zaben su ba kuma an tadadi abun hawa dazai kaisu sabbin rumfunan nasu.

Suma masu sa ido da kula da zaben daga jam’iyyu daban-daban sun nana cewa zaben yana tafiya akan tsari, duk da cewa sun fito daga jam’iyyu daban–daban sun yi fatan Allah ya bama mai rabo sa’a.

Sauran masu kada kuri’a sun sun ce rage yawan cunkuso ya kawo sauki ga masu kada kuri’a kuma tsarin yayi armashi.

Kawo yanzu dai duk harkokin zaben a Najeriya ya tafiya yadda ya kamata ba tare da wani kalubale ba.

Saurari rahoton Hauwa Umar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG