Zaben 2023: Karancin Naira Ya Rage Yawan Sayen Kuru'u

Sabbin kudin Naira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fada a jiya Asabar cewa karancin kudin Naira ya rage yawaitar sayen kuri’u da aka saba gani a zabukan kasar, inda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su karbi kudaden da masu sayen kuri’a suka ba su amma su zabi lamirinsu.

Karancin Naira dai ya haifar da matsaloli a fadin kasar, lamarin da ya sa ‘yan Najeriya da dama suka koka da yadda suka kasa siyan kayan masarufi ko kuma zagayawa. Babban bankin Najeriya dai ya sha suka sosai kan wannan manufa, wadda da dama suka bayyana a matsayin bata lokaci kuma ba a aiwatar da ita ba.

Buhari ya shaida wa manema labarai bayan ya kada kuri’a a Ward A, Sarkin Yara Polling Unit, 003, a Katsina, “Ina sane da cewa babu kudin kamar a can baya da mutane za su rika murde zabe, kamar yadda suka saba yi. Idan kuma sun fitar da kudi, to jama’a su zabi abinda suke so.”

Sabbin kudin Naira

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da huldar jama’a, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Sanarwar mai taken ‘Yan Najeriya sun san muna nufin abin da muke cewa, za su sake zabe mu, inji Shugaba Buhari.

An ambato shugaban na cewa gwamnatinsa ta “rage” al’adar sayen kuri’u. Ya kuma yi alfaharin cewa jam’iyyar All Progressives Congress za ta yi nasara a zabukan gwamnoni da na majalisun jihohi a fadin kasar nan.

Naira

Shugaban ya ce bai yi mamakin sakamakon zaben shugaban kasa ba, wanda ya sa Bola Tinubu ya zama zababben shugaban kasa. Ya ce yakin neman zaben APC na da cikakkun bayanai dalla-dalla.

Ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta zabi shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu, wanda ya taba rike mukamin gwamna na tsawon wa’adi biyu a jihar Nasarawa kuma dan majalisa a majalisar dattawa, tare da gogewar da zai taimaki jam’iyyar.

-Punch